Indiyawan Pima na Arizona sun ce baban kowane mutum da dabbobi shi ne malam-buɗa-mana-littafi, da suke kira Cherwit Make, wanda ya sakko daga gajimare zuwa Shuɗayen Tsaunuka[...] kuma daga gumin jikinsa ne aka halicci mutane. Yayinda mutane suka ƙara yawa, sai suka zamo masu son-kai da kuma faɗace-faɗace, saboda haka sai Cherwit yayi fushi kuma ya yanke shawarar ya nutsar da su bakiɗaya[...]
Akwai wani da ake kira Hauk, hatsabibi dake zaune a tsaunuka, wanda ya sace 'yarsu kuma ya yanka 'ya'yansu maza. [...] Sai ya bi shi a hankali zuwa Wasu Duwatsu na Camfe-camfe; sai ya saka maganin sa maye a cikin barasar da 'yarsa za ta ba shi; sannan, bayan ya sha ta, sai Suha ya bayyana daka wurin da ya ɓuya sannan ya yaudari wawan hatsabibin. [...]
Mutanen Pima sun dogara da wannan almara ta cewa ba za su tsallaka Duwatsun Camfe-camfe ba, domin a nan ne wurin da Cherwit Make yake zaune - yana jiran ɗaukar fansa kan miyagun halayensu domin ya saki gagarumin kogi wanda ke nan kusa.