Indiyawan Pima na jihar Arizona sun ce uban dukkan mutane da dabbobi shi ne malam-buɗe-ido, mai suna Cherwit Make (mahaliccin duniya), wanda ya sauko daga cikin gizagizai yana shawagi zuwa Duwatsun Blue Cliffs […], sannan ya halicci mutane daga gumin jikinsa. Yayin da mutane suka ƙaru, sai suka zama masu son kai da yawan husuma. Saboda haka, Cherwit Make ya ji ƙyamar abin da hannuwansa suka ƙirƙira, kuma ya yanke shawarar nutsar da su gaba ɗaya cikin ruwa. […] Akwai wani mutum mai suna Hauk, wani mugun aljani da ke zaune a cikin duwatsu, wanda yake satar 'ya'yansu mata tare da kashe 'ya'yansu maza. […] Ya bi shi a hankali zuwa cikin tsaunukan Superstition; ya sa guba a cikin ruwan cactus ɗin da 'yarsa za ta ba shi ya sha. Bayan ya sha ruwan, sai Suha ya fito daga inda yake ɓoye, ya kuma farfasa kan wannan mugun aljani wanda ya suma saboda tasirin ruwan. […] Pima sun yi imani da wannan annabci sosai har ba sa kusantar ketare tsaunukan Superstition. Domin a can ne Cherwit Make yake zaune, yana jiran lokacin da muguntarsu za ta kai matuƙarta, domin ya saki wani gagarumin ambaliyar ruwa a doron ƙasa, wanda yake a kulle a bayan jerin waɗannan tsaunuka.  | Entry #39748 — Variant: Kanokanoo
|
Indiyawan Pima na Arizona sun ce baban kowane mutum da dabbobi shi ne malam-buɗa-mana-littafi, da suke kira Cherwit Make, wanda ya sakko daga gajimare zuwa Shuɗayen Tsaunuka[...] kuma daga gumin jikinsa ne aka halicci mutane. Yayinda mutane suka ƙara yawa, sai suka zamo masu son-kai da kuma faɗace-faɗace, saboda haka sai Cherwit yayi fushi kuma ya yanke shawarar ya nutsar da su bakiɗaya[...] Akwai wani da ake kira Hauk, hatsabibi dake zaune a tsaunuka, wanda ya sace 'yarsu kuma ya yanka 'ya'yansu maza. [...] Sai ya bi shi a hankali zuwa Wasu Duwatsu na Camfe-camfe; sai ya saka maganin sa maye a cikin barasar da 'yarsa za ta ba shi; sannan, bayan ya sha ta, sai Suha ya bayyana daka wurin da ya ɓuya sannan ya yaudari wawan hatsabibin. [...] Mutanen Pima sun dogara da wannan almara ta cewa ba za su tsallaka Duwatsun Camfe-camfe ba, domin a nan ne wurin da Cherwit Make yake zaune - yana jiran ɗaukar fansa kan miyagun halayensu domin ya saki gagarumin kogi wanda ke nan kusa. | Entry #39844 — Variant: Not specifiednone
|
'Yan asalin Pima na Arizona na cewa, uban dukkan mutane da dabbobi shi ne malam-b butterfly, Cherwit Make (mahaliccin kasa), wanda ya yi fuka daga cikin gizagizai ya sauka a kan Blue Cliffs [...] kuma daga gumin jikinsa ya halicci mutane. Yayin da mutane suka yawaita, sai suka zama masu son kai da rigima, sai Cherwit Make ya kyamaci aikinsa ya kuduri aniyar nutsar da su duka [...] Akwai wani Hauk daya, wani aljani na duwatsu, wanda ya saci 'ya'yansu mata ya kashe 'ya'yansu maza. [...] Ya bi shi a hankali har zuwa Dutsen Superstition; ya sa magani a cikin giyar cactus da 'yarsa za ta ba shi; sa'an nan, da ya sha ta, sai Suha ya fito daga maboyarsa ya fasa kwakwalwar wannan mugun aljanin da maganin ya bugu da shi [...] 'Yan Pima sun yi imani da wannan annabcin matuka har ba za su ketare Dutsen Superstition ba, domin a can ne Cherwit Make yake zaune - yana jiran kololuwar muguntarsu don ya sako wani babban teku da ke tsare a bayan tsaunin ya mamaye duniya. | Entry #39845 — Variant: Kanokanoo
|